‘Ba mu amince da sauya fasalin Obamacare ba’

Majalisar dokokin Amurka tayi watsi da kudirin yi wa shirin tsohon shugaban kasar, Barack Obama na lafiya da aka fi sani da Obama Care garanbawul.

Hakan ya biyo baya ne bayan wata takardama da aka shafe awanni anayi ewanda takai majalisar har izuwa karfe 2 na daren yau Juma’a. Ana ganin ba karamin cikas ya kawo wa gwamnatin shugaba mai ci a yanzu ba wato Donald Trump.

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo shi ne yadda ‘yan majalisar jam’iyyar shugaban ta Republican da suka hada da sanata John McCain, Lisa Murkowski da kuma Susan Collins  sun taka rawar gani wajen kashe wannan batu a dandamalin majalisar.

Hakan kuwa ana ganin ba karamin cikas ya kawo wa gwamnatin shugaba mai ci, Donald Trump ba.

A halin yanzu dai majalisar tare da shugaba Donald Trump na neman mafita kan batun na lafiya a Amurka.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da BBC Hausa

1151total visits,1visits today


Karanta:  Korea Ta Arewa Ta Yi Sabon Gwajin Makami

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.