Ba Wanda Zai Cire Magu – Osinbanjo

Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace ba wanda zai cire Ibrahim Magu daga mukamin mai rikon Shugaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa tare da yi wa tattalin ariki ta’anti wato EFCC.

Mukaddashin Shugaban ya furta hakan ne a wajen bikin bude sabon ofishin hukumar na gunduma a Kaduna.

Osinbajo, wanda ya sami wakilcin Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya bayyana cewar Magu ya zama tamkar “Abin ban tsoro ga mutane masu cin hanci”.

“Muna da tabbacin cewar Magu zai kai yakin da muke da cin hanci kasa. Don haka zai ci gaba da kasancewa shugaban hukumar EFCC matsawar ina rike da mukamin mukaddashin shugaban kasa, matasawar Muhammadu Buhari ya ci gaba da kasancewa shugaban kasa” a cewar Osinbajo.

Har yanzu akwai tataburza tsakanin bangaren majalisa da kumata zartarwa kan matsayin mukamin Magu. A baya can, Majalisar dattijai ta yi fatali da sunan Magu har sau biyu yayin da aka gabatar mata domin sahalewa.

 

Asalin Labari:

The Cable

339total visits,1visits today


Karanta:  Mafita A Yajin Aikin Likitocin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.