‘Ba Zan Iya Fitowa a ‘Yar Madigo Ba’ – Rahama Sadau

Rahama Sadau tare da Hafsat Abubakar

Jaruma Rahama Sadau tayi ikirarin cewar ba zata iya fitowa a matsayin ‘yar madigo ba a cikin shirin fim kasancewar yin hakan mummunar dabi’a. Sadau ta furta hakan ne a wajen wani taron bajakolin littafai da fasahar hannu mai taken KABAFEST17 wanda gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar a ranar 5-8 ga watan Yuli na wannan shekarar.

Rahama ta kara da cewa wannan mummunar dabi’a ce, kuma yin hakan ka iya sa a jefe ta kamar yadda aka jefi mahaifinta a baya sakamakon rungumar namiji da tayi a cikin a wani faifan bidiyo.

A lokacin da take gabatar da tattaunawar ta da Hafsat Abubakar, Jaruma Rahama ta bayyana cewa ita kam ba matsoraciya bace, illai dai kawai kasancewar tana da dangi da sauran ‘yan uwa wadanda ya kamata ace tana yin taka tsantsan saboda kare musu nasu mutuncin. Ta ci gaba da cewa ta kasance daya tilo wajen yin fice a kafofi daban daban wanda hakan ya janyo mata samun matsin lamba a bangarori da dama.

A karshe tayi nuni da cewa addinin mutum tsakanin sa ne da Mahaliccin sa, don haka babu bukatar ka bayyana shi ga al’umma, kuma hakan bai sanya ta amince da cudanya addini da nishadi ba.

Ta rufe da cewar babu wanda ya tuntube ta kan maganar korar ta da akayi daga masana’antar shirya fina finai ta Kannywood. Kuma wannan shine karo na farko da ta fara tattaunawa akan al’amarin. Inda take cewa faifan bidiyon bashi da mahada da ita wannan masa’anta, domin faifai ne da akayi shi a cikin harshen turanci.

Karanta:  Kannywood: 'Satar fasaha na matukar illata sana'armu'
Asalin Labari:

Muryar Arewa da Shafin Twitter na @chitranagarajan

6925total visits,3visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.