Ba zan sauka daga mukamina ba — Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Satana Bukola Saraki ya bayyana cewa yana nan daram akan kujerar sa ta mulki ba.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a yau Laraba bayan hatsaniyar da aka samu a majalisar dokokin Najeriya a jiya Talata, Sanata Bukola Saraki ya ce zaben shi aka yi kafin ya samu kujerar, ba nada shi aka yi ba.

Saraki ya kara da cewa shi ba ya mutuwar son mulki kamar yadda mutane ke fada, yana mai karawa da cewar da zarar kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisarsa sun kada kuri’ar tsige shi babu shakka zai sauka daga kan kujerar ta sa.

Ya ce babu kashin gaskiya a zargin da ake yi cewar ya hada baki da tsohon shugaban rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) wajen kitsa hatsaniyar da aka yi a majalisar dokokin kasar.

833total visits,3visits today


Karanta:  PDP da APC duka abu guda ne – Ribadu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.