Babu Ja Da Baya a Yaki Da Boko Haram – Kungiyar Maharba

Hadakar kungiyar maharba masu aikin sa kai da yan kato da gora a jihar Adamawa, sunyi ikirarin cewa zasu ci gaba da taimakawa sojoji a yaki da Boko Haram muddin za’a ci gaba da tallafa musu.

Kamar yadda alkalumma ke nunawa, yan sakai na maharba da kuma kato da gora da dama ne suka rasa rayukansu a yaki da Boko Haram, na baya bayan nan ma shine rashin da suka yi na wani fitaccen kwamandan Maharba Bukar Jimeta da akan yiwa kirari da kwamandan mutuwa.

To sai dai kuma duk da wannan rashi da suka yi, yan sakan sun ce ba gudu ba ja da baya a wannan aiki da suke yi muddin za’a kula da su ko iyalansu idan ta Allah ta kasance.

Hajiya Aisha Bakari Gombi, kwamandar mata a kungiyar maharban Najeriya, kuma ta kusa da marigayi Bukar Jimeta tace su a shirye suke su koma daga.

Aisha Gombi wanda ta tabbatar da kudurunsu bayan kashe Bukar Jimeta, ta bayyana cewa zasu ci gaba daga inda Bukar ya tsaya.

Usman Maraneyo, wani tsohon jami’in tsaro ne a Najeriya kira yayi ga gwamnatocin jihohi da su taimakawa yan sakan da kayakin aiki da kuma kulawa da iyalan wadanda aka kashe a fagen daga.

Ya zuwa yanzu rayuka da dama ne suka salwanta ta sanadiyar rikicin Boko Haram, batun da manazarta ke ganin dole a hada hannu idan ana son kwalliya ta biya kudin sabulu.

Asalin Labari:

VOA Hausa

935total visits,2visits today


Karanta:  Ana kwaso yaran da Boko Haram ta raba da Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.