Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Babu sauran cin bashi ga Najeriya – Ministar Kudi

Ministar Kudi, Uwargida Kemi Adeosun, ta yi gargadi a ranar Talata cewar kada na Najeriya ta sake karambanin karbo bashi domin tafi da kasafin kudade, sai dai zai fi kyau ta yi amfani da hanyoyin samar da kudin shiga na cikin gida, domin tallafawa kasafin.

Hakan yazo daidai lokacin da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi osinbajo ke neman hadin kan kamfanoni masu zaman kansu da su tallafawa kokarin gwamnati kan yunkurin da take na mayar da kasar nan nagartacciya. Osinbajo ya bada tabbacin cewar, gwamnatin tarayya na da kudurin canza akalar kasar bikin watanni sha takwas.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya haryana cewar, kalaman da suka fito daga bakin Ministar, ‘yar manuniya ce kan mi’ara koma bayan da gwamnati tayi kan niyyar da take da shi na karbo bashin dala biliyan biyu ($2b) daga Bankin duniya.

Nijeriya, kasar da tafi kowacce karfin arziki a nahiyar Afrika na cikin matsin tattalin arziki a karon farko a shekaru ashirin biyar. Halin da ya tursasa kasar bazama neman bashi daga kasashen waje domin cike gurbin kasafin kudadenta na shekara, wanda ke da niyyar zakulo kasar daga halin wujijjiga da tattalin arzikin ya fada.

 

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, This Day

865total visits,3visits today


Karanta:  Babu Fasfo ga wanda bashi da katin dan kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.