Babu Yadda Boko Haram Zata Habaka Ba Tare da Haramtattun Kudi Ba – Osinbajo

Yayinda yake jawabi a wajen taron kwamitin dake yaki da kudaden haram a yammacin Afirka mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce babu yadda Boko Haram zata habaka daga gari daya har zuwa garuruwa da dama a Nigeria da wasu kasashen ba tare da samun haramtattun kudade ba

Yemi Osinbajo

A wurin taro na goma sha takwas na kwamitin yaki da halasta kudaden haram a yammacin Afirka, Mataimkain Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo yace matsalar halasta kudaden haram na yiwa kasashe irinsu Najeriya barazana.

Farfesa Osinbajo yayi mamakin yadda wata bakar akida da ta samo asali a gari daya ta habaka har ta yadu cikin kasar da wasu kasashen waje ma, musamman kasashen yakin tafkin Chadi. Yace gungun masu safarar kudaden haram suke samar ma kungiya irin ta Boko Haram kudade domin tabbatar da bazuwar akidar kunyiyar. Ya ce ko shakka babu Boko Haram ta samu tallafin kudi daga ciki da wajen Najeriya.

Yushau Aliyu, kwararre kan sha’anin tattalin arziki, yayi fashin baki akan yadda ake aika kudi daga kasa zuwa kasa. Y ace Najeriya ta samu kwarewa wajen fitar wa da shigowa da kudade saboda akwai wakilan masu yin harkokin. Da zara masu shigo da kudi kasa suka gano wani mai son kudi saisu hada baki da shi su shigo da kudin ko ta hanyar jiragen sama ko kuma wata hanyar kana su saka cikin asusun da ake bukata. Ana kuma iya yin anfani da kungiyoyin addini domin cimma irin wadannan burori.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1110total visits,4visits today


Karanta:  Shugaba Buhari Ya Karbi Rahoto Kan Babachir Da Oke

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.