Badaƙalar Biliyan 2.1: Maina Ya Ƙalubalanci EFCC …Ya Ce Yana Bin Gwamnati Bashin Biliyan 159

Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda ya ce bai saci ko ficika ba, sai dai ma tulin bashin da yake bin gwamnatin tarayya na Naira Biliyan 159.

Tsohon Jagoran Fansho, Abdulrasheed Maina ya ƙalubalanci Hukumar EFCC da ta zo a baje zarginsa da ta ke yi kan badaƙalar Naira Biliyan 2.1 a faife. Inda tsohon jagoran fanshon ya ce, a tsarkake yake kuma baya tsoron a yita ta ƙare.

Maina ya yi wannan ƙalubale ne ta hannun lauyansa, Barista Sani Katu, inda ya ce bai saci ko ficika ba, sai dai ma tulin bashin da yake bin gwamnatin tarayya na Naira Biliyan 159.

Sannan kuma ya nemi Hukumar EFCC da ta tsara yadda za su tattauna batun amma a bainar jama’a, ta yadda zai yi tonon silili duk ‘yan ƙasa su ji yadda abubuwan suke.

A ta bakinsa; “A shekarar 2011 muka daƙile satar Naira miliyan 300 da ake sace wa kullum daga hukumar fansho. Haka kuma ashekarar 2011, muka dakatar da satar Naira biliyan 1.04 duk wata. Sannan mun iya hana ci gaba da satar Naira biliyan 52.5 duk shekara daga hukumar Fansho.

“A na iya tunawa cewa daga shekarar 2011 zuwa 2012, hukumar fanshon ta iya dawo da kuɗaɗe da ƙadarorin da sun kai na Tiriliyan 1.63 wanda suke a hannun Hukumar EFCC.

“Wannan abubuwan da aka bankaɗo kuma aka dawo da su haƙƙi ne da ‘yan ƙasa ya kamata su san da su. Ya na da kyau Hukumar EFCC ta daina kawar da hankalin al’umma daga waɗancan kuɗaɗe Naira Tiliyan 1.63, inda suke fake wa da badaƙalar Naira biliyan 2.1. su yi bayanin waɗancan kuɗaɗe tukunna.” Inji shi

Maina ya ƙara da cewa; “Haka kuma daga shekarar 2016 zuwa Yunin 2017, Na saki bayanan da suka dakatar da satar Naira Tiriliyan 1.3 da ake tafkawa duk shekara. Wanda Babban Alƙalin Gwamnatin Tarayya ya tabbatar da haka.”

Karanta:  Ba Wanda Zai Cire Magu - Osinbanjo

Cikin zarge-zargen da lauyan Mainan ya yi, har da batun Babban Lauya Femi Falana, inda ya zarge shi da siyan ɗaya daga cikin kadarorin satan da hukumar Fansho ta ƙwato. A cewarsa, wannan ne dalilin da ya sa Falana ɗin yake ta zuzuta wutar ɓata mishi suna.

Asalin Labari:

Leadership Ayau

1542total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.