Bamusan Inda Ganduje Ya Dosa Ba – Danburam Nuhu Yakasai

Zaka Iya Fada Mana Menene Yasa Magoya Bayan Kwankwaso Da Ganduje Fada?

Kwankwasiyya Kungiya ce mai girmama doka da oda. Bamu fito don muyi fada ba, bamu fito don kai farmaki kan kowa ba.

Abun da ya faru shi ne, mu magoya bayan Kwankwasiyya mun fito yadda muka saba gudanar da bukukuwan sallah da kuma girmama Sarki da taya shi murnar sallah. Amma abin da ya bamu mamaki shi ne ganin cewa magoya bayan Ganduje nada nifaka a zuciyarsu. Sun fito tawaga guda suka farwa mutanenmu.

Tsohon Sakataren Gwamnati da wasu tsofaffin kwamishinoni na gurin inda aka far musu. An jiwa mutane da dama rauni bada wani dalili ba.

Ba zamu bar abubuwa su ringa faruwa haka ba, tuni muka shigar da korafi zuwa gurin Shugaban ‘Yan Sanda da Hukumar ‘Yan Sanda don su gudanar da bincike.

Kuna Zargin Cewa Da Hannun Gwamna A Cikin Harin?

Kwarai kuwa, muna zargin gwamna nada hannu a ciki saboda magoya bayansa ne suka kaddamar da harin. Gashi kuma har yanzu bece komai ba game da harin. Suna da hannu a ciki. Sun kuma san komai.

Lokacin da aka kaddamar da harin, ‘yan sanda na wajen amma babu wanda aka kama. Sunga duk abubuwan da suka faru, amma babu abun da sukayi na hana faruwar hakan.

Amma munyi imanin cewa Shugaban ‘Yan Sanda da Hukumar ‘Yan Sanda zasu dauki mataki. Bayan haka kuma, zamu tabbatar mun kai lamarin Majalisar Tarayya. Dole ne sai anyi hukunci.

Daga cikin matakin da zamu dauka idan ba ayi komai ba shi ne zamuje kotu. Saboda mun san duk wadanda suka kaiwa mutanen mu hari. Zamu iya gane wadanda suka kai mana hari, idan ba ayi komai ba zamuje kotu don bin kadinmu.

Karanta:  Wadanne Hanyoyi ku ke ganin za a bi wajen maganin annobar fyade?

Lokacin da wannan lamarin ya faru, ba a samu kowa cikin mambobin mu da makami ba. Mutane su sani cewa bama nufin kowa da kaidi

Muna da ‘yancin yayata manufofinmu kamar dukkan wani dan Nijeriya kamar yadda Kundin tsarin mulki ya bawa kowa dama. Duk wanda yake tunanin zai iya kaiwa  mutanenmu hari ya kwana lafiya to yasan karyarsa tasha karya. Zamu tabbatar munyi iya bakin kokarinmu a karkashin doka don samarwa mutanenmu ‘yanci.

Kuna Ganin Cewa Zuwa Kotun Shi Ne Zai Warware Matsalar?

Wannan daya ne daga cikin hanyoyin da Kundin tsarin mulki ya shardanta. Idan kana bin kadinka akwai matakan da zaka bi. Don haka zaka iya duk wani abu karkashin doka mutakar dai bazaka kaucewa doka ba. Muna bukatar ‘yancinmu zamuyi iya yin mu don ganin mun sami wannan ‘yanci namu. Wannan kuwa ya hada harda zuwa Kotu domin ganin an hukunta duk wadanda suka aikata wannan. Ya kamata suji ajikinsu don horatarwa.

Ko Akwai Wata Damar Sasantawa?

Ganin yadda suka kai mana farmaki, ba a shirye suke suga an sasanta ba. ‘Yan Nijeriya kamata yayi su san cewa abin da yake faruwa a Jihar Kano ba karamin abu bane don haka zamu bi duk wata hanya don ganin abubuwa sun koma dai dai.

Amma watakila Shugabancin jam’iyya na kasa zai shigo cikin lamarin daga karshe, amma ganin yadda abubuwa ke tafiya a game da lamarin bana jin a shirye suke suga an sasanta.

Ko Kunada Wata Ka’ida Kan Sasantawar?

Wace ka’ida? Bamu muka fara wannan abun ba. Shi ya fara shi, haka kuma bamu san me yake nufi ba. Idan ka kula da kalamansa a bainar jama’a zaka san cewa akwai abin da yake nufi, amma dai ba mu san nufinsa ba.

Karanta:  An kaddamar da sashin "Nigeria for Buhari 2019"

Shugabanmu yaja bakinsa ya rufe akan lamarin bece komai ba tun lokacin da aka fara. Don haka ba maganar mu bada ka’ida bace don ba musan abin da gwamnan yake nufi ba.

Ba Kuda Tunanin Cewa Abubuwan Da Suke Faruwa Zasu Iya Shafar Damar Da Ire-Irenku Magoya Bayan Kwankwaso Keda Ita A Shekara 2019?

Lamarin zabe wani abu ne da ka iya canzawa a ‘yan mintuna. Komai zai iya faruwa nan da minti daya. Don haka baza kayi maganar komai game da shekarar 2019, komai zai iya canzawa, lissafin zai iya canzawa. Koda yaushe ina fadawa mutane cewa mu jira muga zuwan lokacin tukun.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1913total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.