Bankin Raya Afrika Zai Zuba Jarin Bunkasa Aikin Noma a Afrika

Shugaban Bankin Akiwunmi Adeshina wanda ya bayyana haka ya ce za a kaddamar da shirin ne a karkashin shirin bankin mai taken Ciyar da Afirka.

Bankin raya kasashen Afirka ya ce zai zuba jarin Dala biliyan 24 nan da shekaru 10 domin ganin nahiyar Afirka ta bunkasa aikin noma da samar da abinci maimakon dogaro da kasashen duniya.

Shugaban Bankin Akiwunmi Adeshina wanda ya bayyana haka ya ce za a kaddamar da shirin ne a karkashin shirin bankin mai taken Ciyar da Afirka.

Adeshina ya kuma ce bankin yana kokarin ganin ya samarwa manoma kasuwannin da suka dace da za su dinga taimaka wa manoman wajen samun ribar amfanin gona sabanin yadda ‘yan kasuwa ke yi.

A ranar 4 ga Satumba Bankin raya Afrika zai jagoranci wani babban taron nazarin raya Afrika a Abidjan a bangaren wadatuwar abinci da samar da ayyukan yi a fannin noma.

Bankin yana fatar kashe dala tiriliyan 1 zuwa 2030 a karkashin shirin.

Asalin Labari:

RFI Hausa

562total visits,1visits today


Karanta:  Aisha Buhari ta sake komawa London mijinta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.