Bankuna na asarar N2.2bn ga ‘Yan damfara, inji Babban Bankin Kasa

Babban bankin kasa wato (CBN) ya sanar da cewar wani tsarin yarjejeniya tsakanin bankuna na kasa ya bada rahotannin cewar an samu karin korafin kararrakin damfara sama da kashi 1,200 a cikin shekarar 2016, kiyasin wajen biliyan N2.19 idan aka kwatanta da kararrakin da aka shigar a shekarar 2014.

Bayanan baya bayan nan sun yi nuni da cewar an yi hada-hada a shekarar 2016 da ta kai ta 278,744,529 wadda darajar ta kai ta sama da tiriliyon N64.

Duk da cewar akwai karuwar kashi 71 na yanayin girman hada-hadar, akwai kuma karuwar kashi 31 na darajar hada-hadar idan aka yi la’akari da abinda ya faru a shekarar 2015.

Bayanai sun tabbatar da cewar karuwar kaso 82 kan rahotannin damfara da ake samu, ya janyo  asarar kwatankwacin biliyan N2.19 a harkokin bankin. Sai dai an yi kokarin rage damfarar a mizanin kashi 2.7 idan aka kwatanta da alkaluman na shekara 2015.

 

 

 

524total visits,1visits today


Karanta:  Sojin Nigeria sun amsa yin kuskure kan harin Borno

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.