Barcelona: Mota ta afka wa ‘yan yawon bude ido

Mutum 13 ne suka mutu yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata babbar mota ta afka wa masu yawon bude ido a wurin shakatawa na Ramblas da ke garin Barcelona.

‘Yan sanda kasar Spaniya sun ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka gargadi mutane su nisanci dandalin shakatawar a kusa da Placa Catalunya.

Rahotanin da ganau suka yada sun tabbatar da mutane na gudun ceton rai, inda suke neman mafaka a kantinan da ke kusa da wurin da wuraren shan Gahawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hukumomin agaji sun bukaci a rufe tashar mota da ke kusa da wurin da ta jirgin kasa.

Jaridar El Pais ta ce direban motar ya arce da gudu a lokacin da mutane suka yi dafifi don cafke shi.

Wani dalibi mai suna Marc Esparcia dan shekara 20, wanda ke zaune a Barcelona ya shaidawa BBC cewa ya ji wata kara mai karfin gaske, yayin da ya ga mutane suna gudu. Akwai iyalai da dama da ke shakatawa a wurin a lokacin da abin ya faru, kuma wurin shakatawa na Ramblas daya ne daga cikin wuraren da baki ‘yan kasashen waje ke nikar gari don hutawa.

Ya kara da cewa, abin ya yi matukar girgiza shi, ganin yadda lokaci kadan wurin ya yamutse baki daya tamkar ba a halicci farin ciki a fuskokin jam’ar da ke zaune a wurin ba.

”Na firgita sosai, ai ni ma gudu na yi tare da neman fakewa a wani shago da ake sayar da shayi da gahawa na Starbucks.

Kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani da hukumomi suka fitar kan dalilin ko wadanda suka kai harin.

Sai dai masu tada kayar baya na yawan amfani da motocin daukar kaya wajen kai hare-hare cikin bainar jama’a a kasashen turai tun a shekarar da ta wuce.

Asalin Labari:

BBC Hausa

566total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.