Barcelona ta sake sayan Gerard Deulofeu daga Everton

Gerard Deulofeu

Barcelona ta sake sayan dan wasan gefe Gerard Deulofeu daga Everton bisa wata yarjejeniyar da ake ganin ta kai fam miliyan 10.6.

Da farko Deulofeu ya je Everton ne kan aro a kakar 2013-2014, sannan ya rattaba hannu kan yarjejeniyar din-dindin a shekarar 2015.

Dan wasan mai shekara 23 ya buga wa Everton wasanni 13 a kakar bara kafin ya koma AC Milan a watan Janairu.

Dan Spaniyan, wanda ya ke dan makarantar ‘koyon kwallo ta Barcalona da ke Nou Camp ne, ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar shekara biyu.

Bayan ya samu kaka mai kyau a Merseyside, Deulofeu ya bata da kociya Ronald Koeman wanda ya ba shi damar zama a Italiya a kashi na biyu na kakar bara.

Ya buga wasanni 36 da farko, kuma ya buga 39 bayan an fara wasa inda ya sha kwallaye takwas. Da ya cigaba da zama, da kwantiraginsa ya kai watan Yunin shekarar 2018.

Deulofeu ya ce: “Ina matukar farin cikin komawa gida. Ina shaukin in fara wannan aiki. Na dade ina son in kasance a nan.”

Asalin Labari:

BBC Hausa

806total visits,2visits today


Karanta:  Za a gwada lafiyar Lukaku a Man United

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.