Batun Raba Nijeriya Ya Dauki Sabon Salo

  • A Bar Ibo Su Kafa Kasar Biyafara — Matasan Arewa
  • Ba Mu Da Wurin Zuwa — Ibo Mazauna Arewa
  • Har Yanzu Muna Farautar Matasan — el-Rufai

Daga Abdulrazak Yahuza Jere da Mubarak Umar, Abuja

Gamayyar Kungiyoyin Arewa sun yi kira ga mukaddashin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da ya kyale kabilar Ibo su samu cikakken ‘yancin kafa kasar Biyara kamar yadda suke kokarin yi shekaru aru-aru.

Matasan sun bayyana hakan ne a wata takardar da suka aika wa Mukadashin Shugaban Kasa, sannan suka raba wa manema labarai, inda suka ce, Ibo sun dade suna neman ficewa daga kasar nan, saboda haka lokaci ya yi da ya kamata salin alin a kyale su domin su ci gashin kansu.

A cikin wata takardar da suka fitar, mai dauke da sa hannun Ambasada Yerima Shettima, Aminu Adam, Joshua Biashman, Abdul-Azeez Suleiman da Nastura Ashir Sharif, matasan su ce: “Shekaru biyar bayan samun ‘yancin kai, watau 15 ga watan Janairun 1966, wasu daga cikin manyan jami’an soja ‘yan kabilar Ibo suka bayyana tsanarsu karara ga Nijeriya, inda suka jagorancin juyin mulki na farko, wanda daga wannan lokaci tarihin kasar ya sauya baki daya.

“Wannan aika-aika da Ibo suka yi ta janyo asarar miliyoyin mutane ciki har da manya daga Arewa, domin duk wani soja dan Arewa, daga kan mukamin Laftanar Kanal zuwa sama sai da aka kashe shi, ko kuma ya sha da kyar. Har ila yau, suka rushe Gwamnatin Arewa da ta Yamma, amma suka bar tasu ta Ibo yadda take.

“Kamar yadda Ibo suka tsara, Aguiyi Ironsi ya yi amfani da gibin da aka samu, maimakon ya mika mulki ga ragowar wadanda suke cikin gwamnati, wanda a zahiri shi ne abin da ya kamata ya yi, sai ya ayyana kansa a matsayin Shugaba saboda mutanensa.” A cewar su.

Har ila yau, sun kara da cewar abubuwan da suka faru ne ya sanya manyan Sojoji daga yankin Arewa jagorantar kwatar mulki daga hannu Aguiyi Ironsi ko ta halin kaka a 29 ga watan Yuli, 1966. Sakamakon tsokanar ‘yan Arewa da Ibo suka rika yi kan yadda aka kashe Shugabannin Arewa, lamarin ya janyo asarar rayukan miliyoyin kabilar Ibo a Arewa. Wanda bayan Laftanar-Kanal Yakubu Gowon ya zama Shugaba Kasa bisa yarje masa da manyan jami’ai suka yi. Laftanar-Kanal Ojukwu, ya ki amincewa da Gowon a matsayin Shugaba. Kwanaki kadan bayan, Ojukwu ya ayyana fice wa daga Nijeriya domin kafa ‘yantacciyar kasar Biyara a ranar 20 ga watan Mayu, 1967, wanda ya janyo yakin basasa da ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin ‘yan Nijeriya.” In ji su.

Haka zalika matasan sun bayyana cewar tuni Ibo sun janye batun Biyara a ranar 15 ga watan Janairu, 1970, inda Phillip Effiong tare da wasu jiga-jigai a kabilar Ibo suka tunkari Gowon domin sasantawa da batun janye makamai. Amma sai ga shi wasu tsageru sun sake taso da batun.

“Tsakanin shekaru biyu da suka gabata kabilar Ibo sun sake haduwa wuri guda tare da bayyana bukatarsu a fili ta sake kafa kasar Biyara karkashin sabuwar Kungiyar da suka kirkiro MASSOB, wadda Ralph Uwazuruike ke jagoranta. Lamarin ya kara ta’azzara ne lokacin da Nnamdi Kanu ya kaddamar da tasa kungiyar mai suna IPOB, har ma ya bude haramtaccen gidan rediyo ya ci gaba da yada shirye-shirye wadanda ka iya janyo babbar barazana ga zaman lafiyar kasar nan; musamman zagi, cin mutuncin da nuna barazana ga sauran kabilun Nijeriya.

“Abubuwan da Nnamdi Kadu ya rika yada wa sun hada da barazana ga rayuwar wadanda ba Ibo ba da suke rayuwa a yankunan Inyamurai – musamman Yarbawa, Hausawa da Fulani, karara ya nuna sun mallaki makaman kare dangi wadanda za su yi amfani da su wajen aiwatar da shirunsu na rufe hanyoyin Kudu Maso Gabas.

“Kanu da magoya bayan IPOB sun bayyana bai’arsu ga tabbatuwar “Jamhuriyar Biyara” kuma sun  ci gaba da yada mummunar akidarsu a kullum, amma ba a taba samun Shugaba ko da guda daya daga kabilar Ibo ya ja masa kunne ba. Maimakon haka ma, wasu daga cikin manyansu, irin su Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Mista Ike Ekweremadu har gayyatarsa gidajensu suke yi. Duk kuwa da cewa Kanu ya karya dukkan wani nau’in sharadin da aka shimfida kafin a bada belinsa.

Karanta:  An tura ƙarin jami'an tsaro jihar Taraba

Matasan Arewa sun koka matuka kan yadda Shugabannin Ibo suka yi biris da al’amarin Biyara, domin ba sa tsawatarwa ‘ya’yansu kan irin illar abin da ka iya zuwa ya dawo.

Sun ce: “Rahoton da suka fitar game da balahirar, Gwamnonin yankin kabilar Ibo ta hannun Gwamnan Ebonyi, Dabid Umahi, ba su nuna wa Kanu da Uwazuruike kuskurensu ba balle su ja masu kunne. Abin da ma suka nuna shi ne, zanga-zangar da ‘Yan A Waren Biyara’ ke yi ta zaman lafiya ce.

“Tun da wadannan abubuwa suke faruwa, babu shugaba guda daya daga kabilar Ibo wanda ke rike da mukamin siyasa ko na gargajiya, ko kuma wasu jagorori na sauran bangarorin kasar nan ko na kasashen duniya da suka gargadi masu fafutukar kafa kasar Biyara. Dadin dadawa, cikin masu rike da manyan mukamai babu wanda ya fito karara ya nesanta kansa da IPOB ko kuma ya yi tir da ayyukanta, sai baya-bayan nan Gwamna Rochas da ya yi magana biyon bayan Sanarwar Da Muka Fitar a Jihar Kaduna.” In ji su.

Har ila yau, sun nuna cewar dukkan wata ganawa da Osinbajo yake yi da Shugabannin kabilar Ibo ba za ta canza zani ba, kasancewar tun da balahirar ta kunno kai babu mutum guda daga yankin Kudu da ya nesanta kansa da Nnamdi Kanu da magoya bayansa.

“Duba da yadda abubuwa suka faru, hakika mun gamsu cewar lamarin ya sha kan mutanen da suke gurfana a gabanka da sunan tabbatar da zaman lafiya tsakanin kabilar Ibo da sauran kabilun kasar nan, akwai shakku matuka kan fafutukar Ibo da kuma barazanarsu ga Nijeriya.

“Mummunan tanadin da masu fufutukar kafa Biyara suka yi ya shiga zukatan mutanensu da yawa wanda muke ganin da wahala, ganawarka da wasu daga cikin shugabannin Kudu Maso Gabas zai kawo karshen wannan jekala-jekalar musamman idan aka yi la’akari da matsalolin da suka faru a baya.” In ji su.

Baya ga haka, Matasan sun nusar da Mukaddashin Shugaban Kasa cewar Ibo su ne kabilar da aka fi karbar hannu biyu-biyu a Arewa, saboda haka ba za su zuba ido ana ci gaba da yi wa al’ummarsu cin kashi a Arewa ba, saboda haka tarukan sa’a biyu ba zai iya magance matsalar ba.

“Ibo su ne mafi akasarin kabilar da aka fi karbar su hannu biyu-biyu a cikin dukkan kabilun Nijeriya, barazanar da suke yi babu kakkautawa tare da cin mutuncin shugabannin Arewa da al’ummarsu, al’ada da addininsu wanda su ne kiraye-kirayen kafa Biyafara ya fi tasawa a gaba zai yi wahalar magancewa ta hanyar tarukan da aka yi na sa’o’i biyu kacal. In ji su.

Matasan su ce: “Domin tabbatar da haka, ‘yan sa’o’i bayan taro da ka yi da shugabannin yankin Kudu-Maso-Gabas, ‘Yan Biyafara sun ce babu ruwansu da shugabannin kuma suka nesanta kansu da taron.

Har ila yau sun koka matuka bisa ikirarin da Nnamdi Kadu ya yi cewar sun mallaki makaman kare kansu a duk lokacin da suka bukaci ballewa.

“Wani abin ban takaicin shi ne, Kanu ya fito fili ya yi ikirarin cewa ‘Yan Biyafara suna da isassun makamai da za su yi yakin ballewa wanda akwai kamshin gaskiya a maganar idan aka yi la’akari da irin miyagun makaman da ake fasa-kwaurin shigowa da su kasar nan tun daga 2009 kuma a wasu lokuta mahukuntan Nijeriya sun sha kwacewa, da aka bi diddiginsu an ta’allaka su da Ibo.

“Lamarin ya cigaba da yin kamari tare da daga hankalin jama’a kuma ba za a lamunci hakan ba – musamman yadda shugabannin siyasa da kungiyoyi na Ibo suke fitowa fili baro-baro suna halasta zage-zage, cin mutunci, barazana, nuna kiyayya da neman tada zaune tsaye da ‘Yan Biyafaran da Nnamdi Kanu ke wa jagoranci suke yi a kan Arewa da kuma Nijeriya baki daya.

Karanta:  Gwamnatin Nigeria ta Ayyana 'Yan IPOB a Matsayin 'Yan Ta'adda

“Har ila yau, maimakon tsawatarwa, sai ga shi shugabannin Kudu-Maso-Gabas cikin zumudi sun rungumi Kanu, sun amince da shi tare da shirya ma sa abubuwa daban-daban na girmamawa.” A cewarsu.

Haka zalika matasan sun zayyana matakan da ya kamata gwamnati ta dauka tun da har su Ibo da kansu sun bayyana karara suna dauke da makamai a hannunsu, a cewarsu, rashin daukar mataki babbar barazana ce ga zaman lafiyar Arewa.

“Bisa yadda ‘Yan Biyafara suka amsa cewa sun shirya tsaf da makamai domin ballewa cikin tashin hankali, muna da yakinin cewa hakan yana da matukar hadari ga sauran sassan kasar nan musamman Arewa idan muka cigaba da basarwa tare da zama da Ibo ba tare da fargaba ba, ganin cewa sun bazu a cikin lunguna da sakunan al’ummominmu.

“Kuma tunda ya bayyana cewa Ibo ba su saduda da abin da suka rikito wa kansu na yakin basasa da aka malalar da jini a shekarar 1966 ba, muna matukar nuna damuwar cewa ba za su taba gamsuwa da komai ba in ba tabbatar da musu da Biyafararsu ba.

“Sannan tunda yake Ibo sun shiga duk wani lungu da sakon Arewacin Nijeriya inda aka karbe su hannu biyu-biyu, a matsayin masu kishi, mun yi amannar cewa yankin ba zai cigaba da kasancewa cikin zaman dar-dar tun da suna yi wa mutane barazana kuma bisa cewa tun da dadewa Ibo sun yi nisa wajen tabbatar da a yankin Kudu-Maso-Gabas ba a bar ‘Yan Arewa da ‘Yan Kudu-Maso-Yamma sun samu ‘yancin mallakar duk wani wurin kasuwanci ba alhali a Kano kawai, suna da shaguna sama da 100,000 a kasuwanni.

“Tunda matasan Nijeriya su ne suke da yawan da ya kai kashi 60 a cikin 100, fatanmu shi ne su gaji kasar nan cikin yanayi mai kyau domin su cigaba da gina ta saboda ingantuwar rayuwarsu da ta ‘ya’yansu da za a haifa nan gaba amma ba a mummunan yanayi na tada-zaune-tsaye, muguwar kiyayya da gaba da kuma mugun halin da Ibo ‘Yan Biyafara ke ta kokarin kakaba mana da karfin tsiya ba.

“Domin kara dagula lamarin ma, shugabanninsu suna cigaba da goyon bayan yunkurin na cin amana kuma wannan ya haifar mana da damuwar cewa duk abin da suke fada a kanmu da gaske suke kuma sun daura niyyar yi – “a kashe kowa da kowa a Gidan Zoo” wato (Arewa).

Saboda haka Matasan sun fitar da mafita wadda suke ganin ita ce maganin wannan fitinar ta raba kasa a fitar da Biyafarar da ake kiraye-kiraye yanzu daga Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya cikin kwanciyar hankali da lumana ita ce, watau a dauki matakan da za su kai ga kafa Kasar Biyafara daidai da tsarin cin gashin kai kamar yadda yake kunshe a dokar Majalisar Dinkin Duniya.

Tsarin cin gashin kai tun daga yakin duniya na biyu ya kasance wani bangare na yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya wadda a karkashin Makala ta 1, karamin sashe na 2, ya ce daya daga cikin manufar kafa Majalisar Dinkin Duniya ita ce “samar da kyakkyawar alaka a tsakanin kasashe bisa tsarin girmama ‘yancin juna da cin gashin kan mutane.

“Muna bayyana cewa wannan tsarin ya ayyana cewa mutanen kowace kasa suna da ‘yancin neman cin gashin kai, kuma tun da yarjejejiniyar ba ta shardanta wasu dokoki da dole kasashe za su bi kan hakan ba, kenan duk kankantar kabila tana da ‘yancin ballewa ta kafa kasar kanta.

“Wannan tsarin na neman cin gashin kai an kara sanya shi a cikin yarjeniyoyin kasashen duniya guda biyu: Yarjejeniyar Majalisa Dinkin Duniya kan ‘Yancin Tattalin Arziki, Walwala da Al’adu da kuma Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan ‘Yancin Fararen Hula da Siyasa. Makala ta 1 kan yarjejeniyoyin guda biyu sun karfafa tare da kare ‘yancin mutanen da suke neman cin gashin kai. Kasashen da suka rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin an dora masu nauyin tabbatar da wannan ‘yancin, kasancewar yana karfafa dokar duniya da ta bawa mutane damar neman ‘yancin gashin kai.

“A sakamakon yadda masu kiraye-kirayen ballewa na Ibo suka yawaita tare da yin barazanar abin zai dauki sabon salo, muna bayyana cewa akwai bukatar tabbatar da cewa an basu dama su nemi ‘yancin cin gashin kansu kamar yadda yake kunshe a cikin yarjejeniyoyin duniya da muka lissafa a sama wanda Nijeriya ta rattaba hannu a kai.

Karanta:  Bama Bukatar Wani Sabon Yakin - Ohanaeze Ndigbo

Daga karshe, sun bukaci Mukaddashin Shugaban Kasa da ya dubar cewar, abu ne da ba zai yiwu ba a yi tunanin cewa sauran al’ummar kasa za su zuba ido suna kallon wata kabila kwara daya tak tana abin da ta ga dama da suka hada da barazana, tada zaune tsaye, cin mutunci da kiraye-kirayen yaki ba tare da an ce mata uffan ba.

Saboda haka su bukaci cewar lokaci ya yi da za a ba Ibo damar tattara kayansu domin su kafar kasarsu ta Biyara.

A wani labarin mai kama da martani kuma, kabilar Ibo mazauna Arewacin kasar nan sun fitar da sanarwar mai dauke da bayanan cewar ba za su fice daga yankin ba kamar yadda Gamayyar Kungiyoyin Arewa suka bukata, domin ba su da wani wuri da wuce Arewa, inda suka ce suna da cikakken ikon zama a yanki duba da dadaddiyar dangantakar da ke tsakaninsu da al’umma mazauna Arewa, musamman Hausawa da Fulani.

Shugaban tawagar Ibo mazauna Arewa da suka hada jihohi 19 da Abuja, Cif Chikezie Nwogu ne ya yi wannan furuci yayin ziyarar da ya jagorancin masu rike da mukaman gargajiya suka kai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai.

Ibon sun koka matuka sakamakon kiraye-kirayen da ake yi na rabar kasar, inda suka bukaci a ci gaba da zama lafiya a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Nwogu ya gode wa Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin Kaduna bisa jajircewa da suke yi wajen tabbatar ganin zaman lafiya ya samu tabbatuwa a fadin tarayyar kasar nan.

Ya ce: “Mun zo Kaduna don mu gana kan abubuwan da suke faruwa yanzu haka a Arewa, wadanda suka shafi wa’adin da Matasan Arewa suka bawa kabilar Igbo da kuma martanin da ‘yan kungiyar IPOB suka yi ga matasan, wanda ka iya janyo rikici mai hadarin gaske. Ba mu yi don mu yi Allawadai da kowa ba, illa iyaka mu yi godiya ga Gwamnan el-Rufai, Gwamnonin Arewa da kuma Gwamntanin Tarayya bisa matakan da suke dauka na kawo karshen wannan balahira.”

“Muna fatan gwamnati za ta yi waiwaye domin shawo kan matsalar ‘yan a ware da kuma barazanar wa’adin Matasan Arewa ga kabilar Ibgo.” A cewar Nwogu.

Da yake nasa tsokacin, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya ce yana da cikakken iko, da yawun Gwamnonin Arewa karkashin Gwamnan Borno, Kashim Shettima, na tabbatar wa da Ibo cewar su kwantar da hankalinsu, babu abin da zai same su a Arewa.

Har ila yau, Gwamnan ya jadadda cewar komai daren dadewa, za a kame matasan da suka bawa Ibo wancan wa’adi domin gurfanar da su gaban kuliya.

Gwamnan ya ce: “Jihar Kaduna ta kowa ce, sam ba mu da bambanci. Muna yi wa Ibo maraba da zuwa Kaduna, su kwantar da hankalinsu, babu abin da zai same su.

“Kaduna ta yi fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini, duk da cewa kafin faruwar wadannan abubuwa ta kasance gida na kowa, ana zaune lafiya ba tare da bambanci ko fargaba ba, saboda haka ba zamu aminceta zama dandalin rikici ba.

“A bisa ikona na Gwamna, na soke batun bangaranci, duk wanda yake zaune a Kaduna, kawai dan Kaduna ne, babu bukatar shaidar takardar zama dan jihar nan. Mun kama mutane da yawa wadanda suke ingiza al’umma su yi rikici. Saboda haka ina kara tabbatar maku da cewa, komai daren dadewa za mu kama matasan da suka yi wancan ikirari.” In ji Gwamna el-Rufai.

Asalin Labari:

LEADERSHIP Hausa

1003total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.