Bayan Goguwar Nan Ta Hurricane Harvey, Yanzu Kuma Wata Goguwar Da Ake Kira Irma Ta Afkawa Kasar Amurka

Duk da cewa ba a gama murmurewa daga barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Hurricane Harvey tayi ba, yanzu haka kuma wasu jihohin da yankunan kasar Amurka na fuskatar wata sabuwar annobar guguwa da ake kira Hurricane Irma a cewar Hukumar Kula da Guguwa ta Amurka ranar Litinin.

Guguwar Hurricane Irma mai karfi ce korai inda takai mataki na 4  a ranar litinin, ba tare da bata lokaci ba garuruwan Florida da Puerto Rico suka saka dokar ta baci saboda tasirin da kuma abinda goguwar zata haifar.

Tuni Gwamnan Jihar Florida Rick Scott ya sanya dokar ta baci bayan da guguwar ta Irma ta bar mataki na 3, inda ake jira ko masu hasashen yanayi zasu ce goguwar zata iya haifar da zabtarewar kasa a Florida.

Anyi hasashen guguwar zatayi karfi mutuka ranar Talata kuma zata isa zuwa Puerto Rico ranar Laraba a cewar Hukumar Kula da Guguwa ta Kasar Amurka

“Duk da damfar tattalin arzikin da ake fama dashi a Puerto Riko, an sami ware dala miliyan 15 domin shirin ko-ta-kwana”, a cewar gwamnan Puerto Rico, Ricardo Rosselló.

Rosselló yake cewa yankin da keda yawan mutane miliyan 3.4 an samar da mutsugunin ko-ta-kwana guda 456 wanda zai iya daukan mutum 62, 100.

Jami’an gwamnati tuni suka kyayade farashin abubuwan da suka zama dole nemansu kamar abinci, ruwan sha, magani, jannareto dama batira.

Goguwar Hurricane ta jawo zabtarewar kasa a jihohin Texas sati guda da ya wuce wanda yayi sanadiyar mutuwar mutune 50.

Mutum kusan 43,000 yanzu haka na boye a gidajen karkashin kasa, yayinda annobar guguwar ta shafi gidaje 156,000.

Karanta:  Wani soja ya fado daga jirgi mai saukar ungulu a Belgium
Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

681total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.