Bazamu Janye Dakarunmu Ba Daga Abia- Rundunar Sojin Najeriya

Mai Magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya ce, babu kamshin gaskiya a game da janye dakarunsu.

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta a karkashin shirin Operation Python Dance da aka kaddamar don magance miyagun ayyuka a yankin kudu maso gabashin kasar.

Rundunar ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da sanarwar da gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya fitar, wadda ke nuna cewa, za ta janye dakarunta da ake aiki a karkashin shirin Operation Python Dance II.

Mai Magana da yawun rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya ce, babu kamshin gaskiya a game da janye dakarunsu.

A ranar Alhamis da ta gabata ne, gwamna Ikpeazu ya ce, rundunar za ta fara janye sojojin daga titunan unguwannin jihar Abia a yau Jumma’a.

Za a ci gaba da gudanar da shirin har zuwa karshen shekara kamar yadda Sheka ya tabbatar.

Shirin ya kunshi yaki da masu garkuwa da mutane da fashi da makami da kashe-kashe da kuma yaki da miyagun ayyukan masu kokarin raba kan kasa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

524total visits,2visits today


Karanta:  Babu inda 'yan kabilar Igbo zasuje - Ganduje

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.