Beyonce: Hoton Sir Carter da Rumi Ya Bayyana

Mawakiya Beyonce ta fitarda hoton ta rike da tagwayen ta a karo na farko tun bayan haihuwar su.

Fitacciyar mawakiyar ta kasar Amurka ta tabbatar da sunayen su a matsayin Sir Carter da kuma Rumi wanda akayi ta raderadi a kafafen sada zumunta bayan ita da maigidan ta wato Jay-Z sun shigar da sunayen domin yin ragistar hakkin mallakar su.

Hoton dai ya nuna mawakiyar ‘yar shekara 35 mai ‘ya’ya uku a halin yanzu rike da ‘yan tagwayen a cikin wani zani mai launin Pupple da kuma shudin mayafi.

Hoton na Sir Carter da Rumi wanda mahaifiyar su ke rike dasu ya samu kutsawa fiye da miliyan tara a shafin sadarwa na Instagram inda ta rubuta Sir Carter da Rumi sun cika wata guda a yau.

Sir Carter and Rumi 1 month today. ??❤️??????????

A post shared by Beyoncé (@beyonce) on

Beyonce da mai gidan ta Jay-Z sun kasance iyayen yara uku wadanda suka hada da babbar ‘yar su mai suna Blue Ivy.

Hoton da Beyonce ta wallafa a shafin na ta na Instagram wanda take tsaye a wani lambu yana kamanceceniya da irin wanda ta tafa wallafawa a lokacin data sanar da samun juna biyu da tayi a watan Fabrairu na 2017.

Hoton na sanarwar samun juna biyu na Beyonce ya samu zarta duk wani hoto da aka taba sakawa a Instagram farin jini.

Asalin Labari:

Muryar Arewa da Shafin Twitter da BBC News

2712total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.