BOKO HARAM: Amurka Ta Sake Alkawarin Taimaka Ma Najeriya

Wata tawagar jami'an Amurka ta sake karfafa ma Najeriya gwiwa ta wajen sake yin alkawarin taimaka ma ta a yaki da Boko Haram.

Yayin da kungiyar Boko Haram ke zafafa hare-harenta a arewa maso gabashin Najeriya, Amurka, wadda a baya ta sha alwashin taimaka ma Najeriya, ta kuma sake alkawarin taimaka ma Najeriya a cigaba da yakin da ta ke yi da Boko Haram. Wata tawagar jakadan Amurka a Najeriya ce ta yi alkawari na baya-bayan nan, a yayin da ta kai ziyara ga jami’an soji a birnin Maiduguri.

Bayan ganawar sirri da su ka yi da sojojin Najeriya, said an Majalisar Dattawan Amurka Senator Christopher Coons, wanda da shi da Jakadan Amurka a Najeriya su ka jagoranci tawagar mai mutane 6, ya shaida ma ‘yan jarida wannan albishir din tare kuma da cewa tawagar ta gamsu da irin bayanan da sojojin Najeriya su ka yi ma ta da kuma irin kokarin da su ke yi, saboda haka, in ji shi, Aurka za ta agaza ma Najeriya.

Daga bisani kuma shi Manjo-Janar Ibrahim Attahiri mai kula da yankin na arewa maso gabashin Najeriya ya yi karin haske ma ‘yan jarida ya na mai cewa sun gabatar da bukatar jiragen yaki da motoci masu sulke da sauran makaman yaki ga Amurkawan kuma sun yi alkawarin taimakawa. Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton:

Asalin Labari:

VOA Hausa

428total visits,2visits today


Karanta:  Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Leave a Reply

Your email address will not be published.