Buhari bai iya mulki ba — Shekarau

Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bata tabuka wani abun azo a gani ba a tsawon fiye da shekara uku da ta yi kan mulkin kasar.

Malam Ibrahim Shekarau, wanda ke neman jam’iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a zaben 2019, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin Buhari na tafiyar da mulki “tamkar ba ta san abin da take yi ba”.

“Hatta wadanda suke adawa da gwamnatin sun yi mamakin yadda ta gaza wurin aiwatar da abubuwan da ta yi alkawari,” in ji Shekarau, wanda a baya ya yi tafiyar siyasa tare da Shugaba Buhari.

Ya kara da bayyana rawar da gwamnatin ta taka da cewa ba yabo ba fallasa.

Sai dai ana ta bangaren, gwamnatin APC tana bugar kirjin cewa ta farfado da tattalin arzikin kasar, wanda jam’iyyar PDP ta “ruguza” a shekara 16 da ta shafe tana mulki.

Sannan ta ce ta sanya kasar a kan turbar dogaro da hanyoyin samun kudaden shiga daban da man fetur.

A ‘yan kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana aniyarsa ta neman wa’adi na biyu a zabe mai zuwa.

Sai dai wasu masana na ganin zai fuskanci zazzafan kalubale ganin yadda wasu jama’a da dama suka dawo daga rakiyar yadda ya ke gudanar da gwamnatinsa.

Tsohon gwamnan jihar ta Kano ya ce zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama shugaban kasar.

Ya kuma musanta zarge-zargen cewa yana da hannu a rarraba kudaden da ake zargin an wawure gabannin zaben 2015.

Har yanzu dai rahotanni sun nuna cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na bincike kan lamarin, amma ba su kai lamarin gaban kotu ba.

Karanta:  Na dade da daina karbar kudin fansho daga Kwara - Saraki
Asalin Labari:

BBC Hausa

1754total visits,5visits today


One Response to "Buhari bai iya mulki ba — Shekarau"

  1. Ibrahim Jogana   May 19, 2018 at 10:03 pm

    She tsohon gwamnan kano ya mana bayani akan KUDIN MAkaMAI DIN tukuna kaminnan yace komai game da gwamnatin Buhari.

    Reply

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.