Buhari Ya Bada Damar Gina Layin-Dogo Daga Kano Zuwa Daura Kasarsa Ta Haihuwa

Layin-Dogon zai tashi daga Kano zuwa Karamar Hukumar Jibiya cikin Jihar Katsina, kamar yadda Ministan Sufuri, Rotimi Ameachi ya bayyana.

Amaechin ya bayyana wannan labarin ne a Abuja ranar Juma’a  wajen wani taro da aka gudanar kan tattalin arzikin kasa da tasirinsa ga masu karamin karfi.

Majiyar Cable ta Ambato Amaechi na cewa layikan-dogon da aka sahale a gina sun hada da wanda zai tashi daga Fatakol zuwa Maiduguri, Kano zuwa Maiduguri, Makurdi zuwa Jos, Gombe zuwa Yobe zuwa Borno da kuma Jigawa zuwa Jamhuriyar Nijar.

 

Vanguard 25/08/2017

939total visits,2visits today


Karanta:  Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.