Buhari Ya Jaddawa Shugabannin Hukumomin Tsaro Su Kara Kaimi Wajen Kare Kasar

Yayinda ya gana da manyan jami’an tsaron Najeriya shugaban kasa Buhari ya sake jaddada masu bukatar su kara kaimi wajen yaki da ta’addanci domin su kare kasar da al’ummarta da dukiyoyinsu kuma batun raba kasa ma bai taso ba.

Baban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Abayomi Olonisakin shi ya yiwa ‘yan jarida bayanin sakamakon tattaunawarsu da shugaban kasa.

Yana mai cewa batun tsaro da duk abubuwan dake yiwa tsaro barazana an tattaunasu, kama daga satar mutane da rikicin manoma da makiyaya zuwa batun ‘yan aware irin na Biafra duk sun tattauna, inji hafsan hafsoshin.

Shugaba Buhari ya basu umurni akan abubuwan da ya kamata su maida hankalinsu a kai sosai domin su samu nasarar aikace aikacensu a kasar.

Shugaban kasa yace kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalla ba abun da za’a yi muhawara a kansa ba ne. Dole ne sojoji su yi aiki su tabbatar da kasar ta cigaba da zama kasa daya.

Alhaji Bello Arabi Sardaunan Damaturu daya daga cikin dattawan arewa maso gabashin Najeriya yana mai cewa ganawar da shugaban yayi gaskiya ce bisa ga yin la’akari da abubuwan dake faruwa a kasar. A yi maganin barazanar da ‘yan Najeriya ke yiwa juna a samu a zauna lafiya.

1680total visits,2visits today


Karanta:  Shugaba Buhari ya nemi gafarar 'yan majalisa kan hana su ganinsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.