Buhari Ya Yi Kuskure da Korar Abdulrasheed Maina Daga Aiki -Lauya

Yayin da ake cigaba da cece-kuce game da sake korar tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga shirin fanshon Najeriya, Abdulrasheed Maina daga aiki, masana harkar sharia a kasar sun bayyana cewa akwai kuskure a korar da shugaba Buhari yayi

Shi dai shugaba Buhari, a wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaban kasar na Twitter, ya bada umurnin a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda aka yi ya koma aikin gwamnati.

Har-ila yau shugaba Buhari ya umarci shugabar ma’aikatan gwamantin tarayya, Oyo-Ita Winifred Ekanem, da ta mika rahoton binciken ga ofishin shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Abba Kyari akan lamarin.

To sai dai masana harkar sharia a kasar irinsu Barrister Sunday Joshua Wigra, wani lauya mai zaman kansa a kasar, na ganin akwai gyara a wannan kora ta Mainan.

Asalin Labari:

VOA Hausa

673total visits,1visits today


Karanta:  Nigeria: Evans Ya Amsa Lafinsa Na 'Satar Mutane' a Kotu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.