Buhari ya yi waya da tsohon shugaban APC Bisi Akande

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa tsohon shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Cif Bisi Akande wayar tarho.

Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a birnin London, ya yi wa Cif Akande ta’aziyya bisa ga rasuwar matarsa Madam Omowunmi Akande.

Wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar ta ce a wasikar da shugaban kasar ya rubuta da kansa ranar Laraba bayan ya kirawo Cif Akande ta waya, ya ce:

“Na yi bakin cikin samun labarin mutuwar Madam Omowunmi Akande da wannan safiya. Na rubuta wasikar jaje bayan wayar da muka yi da shi.”

“Rasa matar da mutum ya kwashe shekara 50 da ita, wacce ke matukar kaunarsa, da ke tare da shi komai runtsi, abu ne da zai jijijiga mutum. Ina mika ta’aziyya ta ga daukacin iyalin Akande da abokansu bisa wannan babban rashi da suka yi”, in ji Shugaba Buhari.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar mai dakin Cif Akande, ciki har da mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo.

Cif Akande ne shugaban farko na jam’iyyar APC, wanda ya yi fafutika wajen ganin tsofaffin gwamnonin wasu jihohi na PDP mai mulki a wancan lokacin, wadanda suka samu sabani da jam’iyyar, sun koma APC.

Tun da shugaban ya bar kasar dai bai sake bayyana a bainar jama’a ba.

Kuma kawo yanzu ba a bayyana cutar da yake fama da ita ba.

Sai dai ya gana da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a ranar Talata a birnin na London, abin da ya sa wasu ke ganin alamu ne na cewa ya fara samun sauki.

Karanta:  Nigeria Za Ta Fara Taso Keyar Masu Laifi Su Gudu UAE

Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

  • 19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
  • 5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
  • 10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
  • 26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
  • 28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
  • 3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
  • 5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
  • 7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya

 

Asalin Labari:

BBC Hausa

760total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.