Buhari zai ziyarci London daga Amurka

Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi izuwa birnin New York dake kasar Amurka domin halartar taron Kwamitin Koli na Majalisar Dinkin Duniya, karo na 72 wanda sauran shuwagabannin duniya zasu halarta.

A wata sanarwa da babban mai bawa shugaban kasa shawara a harkar sadarwa, Mista Femi Adesina ya fitar itace shugaban zai halarci tattaunawa ta musamman a wani bangare na Majalisar Dinkin Duniya gami da gabatar da jawabi kan kasa Najeriya.

Taken taron muhawarar na bana itace: ‘Mayar da hankali kan mutane: Kokarin samun zaman lafiya da kuma Rayuwa mai kyau ga kowa da kuma duniya mai cike da nutsuwa.’

Shugaba Muhammadu Buhari zai hadu da shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres wanda zai karbi bakuncinsa inda kuma zai samu ganawa da shugaba Donad Trump na kasar Amurka.

Ana saka ran shugaban zai ziyarci birnin London bayan ya kammala taron na Majalisar Dinkin Duniya.

1976total visits,1visits today


Karanta:  Kishin kasa ne ya sa na karbi mukamin minista — Okonjo- Iweala

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.