Burin Kwankwaso Na Tsayawa Takarar Shugaban Kasa Na Daga Cikin Abin Da Ya Haifar Da Baraka A Kano – Sanata Barau

Shugaban Kwamitin Manyan Makarantu da Asusun Talafawa Manyan Makarantu TETFUND, Sanata Barau Jibrin (APC Kano) a wata hira da yayi ya bayyana wasu dalilai guda biyu wadanda suka saka za a cigaba da samun rashin fahimta tsakanin Kwankwaso da Ganduje

Menene Yasa Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje Yaki Ci Yaki Cinyewa?

Abubuwa ne guda biyu wadanda suka jefa mu cikin yanayi marar kyawun da muka tsinci kanmu a ciki a Kano. Na farko dai ya faru ne tun lokacin da mahaifiyar gwamna mai ci yanzu ta mutu, gwamna mai barin gado yazo ta’aziyya. Lamari marar  kyau ya faru ga gwamna. Lokacin da aka gudanar da bincike sai aka gano cewa duk abubuwan da suka faru sun faru ne saboda rashin katabus daga gurin shugaban jam’iyyar APC na Kano na wancan lokacin.

An sami Shugaban Jam’iyyar na wancan lokacin, Umar Doguwa bai cancanci da mukamin ba. Wannan kuwa doriya ne kan wasu laifuffukan da ake zargin Doguwan da aikatawa. Inda aka gudanar da zaben rashin amincewa da Doguwan aka kuma sauke shi daga mukaminsa. Aka samar da sabon shugaban jam’iyya amma tsohon gwamna Kwankwaso yaki amincewa da canjin shugabancin ya kuma kafe akan hakan. Har yanzu ba a kai ga warware wannan matsalar ba haka kuma wannan na daya daga cikin musabbabin rashin fahimtar.

Abu na biyu kuwa shi ne, kowa yasan gwamna Ganduje mai goyon bayan Shugaba Buhari ne ya kuma bayyana jajurcewarsa da goyon bayansa ga Shugaba Muhammadu Buhari har takarar shekarar 2019. Ya riga ya bayyana hakan a zahiri. Gashi kuwa ga dukkan alamu kai kawon da Kwankwaso keyi gari zuwa gari na nuna cewa shima zaiyi takarar shugaban kasa a shekarar 2019. Masu lura da al’amura na ganin cewa wannan ma na daga cikin abin da ya jawo sabani tsakanin Kwankwason da Ganduje.

Karanta:  Atiku ya kalubalanci masu cewa ya yi sata su ba da hujja

In har akwai wani kokarin warware wadannan matsalolin, to da kuwa an sami zaman lafiya. Amma har idan wani zai cigaba da nuna turjiya akan abinda jam’iyya ta zartar a bangaren magoya bayan Kwankwaso to kuwa za ayi ta samun wannan matsalar.

Amma An Ce Anata Sabanin Ta Karkashin Kasa Tun Kafin Lokacin Zuwa Ta’aziyyar Mahafiyar Gwamnan?

Ban san komai ba game da wannan. Bana san bancike kan cece-kuce. Bana tsammanin akwai wata matsala kafin wancan lokacin. Wadannan batutuwan biyu kawai su ne dalilan.

Ta Yaya Za A Magance Wannan Matsalar?

Tuni jam’iyya ta dauki mataki, haka kuma duk wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun amince da matakin jam’iyyar sai dai ‘yan Kwankwasiyya ne kawai suka ki amincewa da matakin. Wannan ita ce matsalar.

Wane Kokari Masu Ruwa Da Tsaki Irinku Sukeyi Don Magance Sabanin?

Babu wani abun da zamu iya face ummartar dukkanin ‘yan jam’iyya suyi biyayya ga matakin jam’iyya. Matakin jam’iyya shi ne mafi rinjayi. Dole ne mu tsaya akansa.

Mutane Da Dama Nada Yakinin Cewa Wannan Sabanin Na Iya Shafar Makomar Jam’iyyar APC A Kano A Zaben Shekarar 2019?

Bazaka taba raba siyasa da rigingimu irin wannan ba. Kana warware wani, wani na tasowa amma dai a karshe jama’a dake kaunar jam’iyyar da Jihar Kano zasu yarda a sulhunta. Kalli abin da ya faru a Legas a shekarar 2015 tsakanin Fashola da Tinubu. Sunada mabanbantan ‘yan takarar gwamnan jihar amma dai a karshe lokacin da Ambode wanda Tinubu ke marawa baya ya zama sahihin dan takarar APC a jihar sai shi Fashola ya mara masa baya.

Karanta:  Hukumar zaben Nigeria ta fara shirin kiranyen Melaye

Haka nan abin da ya faru a jihar Adamawa lokacin da Atiku Abubakar ya tsaya takarar shugaban kasa, ya fadi a takarar cikin gida hakama dan takararsa na gwamnan jihar Adamawa ya fadi. Amma duk da haka yayi watsi da shirinsa na farko ya bi jam’iyya. Don haka banga wata matsala a shekarar 2019 ba in dai har ra’ayin jam’iyyar ne da Kano a gaban mu.

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

9053total visits,4visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.