Burnley ta dauki mai tsaron raga Anders Lindegaard

Burnley ta dauki tsohon mai tsaron ragar Mancherster United Anders Lindegaard bisa yarjejeniya zuwa karshen kakar wasannin bana.

Mai tsaron ragar Burnley din Tom Heaton na murmurewa daga tiyatar da aka yi masa a kafada, lamarin da ya sa Nick Pope ya maye gurbinsa na wucin gadi a wasa biyu na baya-bayan nan da suka kara.

“Zan yi iya kokarina na kuma nuna bajinta a bangaren tsarar raga, domin wuri ne da yake bukatar kula da mayar da hankali, kuma nayi farin-ciki da kasancewa a wurin”. In ji Dan kwallon.

Lindegaard ya yi mako guda yana atisaye a kulob din kafin ya koma.

Asalin Labari:

BBC Hausa

258total visits,3visits today


Karanta:  Madrid ta Lashe Kofin gasar Spanish Super Cup

Leave a Reply

Your email address will not be published.