‘Cigaban Afirka ne Kawai Zai Magance Matsalar Bakin-Haure’

Shugabanin kasashen Nijar da Chadi sun bayyana cewa, cigaban kasashen Afirka ne kawai, zai magance yadda matasa ke barin kasashen nahiyar suna tafiya Turai suka da tarin hadurran da ke tattare da hanyoyin da suke bi.

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou yayin gaisawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadar gwamnati da ke birnin Paris, 28 ga watan Agusta, 2017. Shugabanin kasashen Nijar da Chadi sun bayyana cewa, cigaban kasashen Afirka ne kawai, zai magance yadda matasa ke barin kasashen nahiyar suna tafiya Turai suka da tarin hadurran da ke tattare da hanyoyin da suke bi.

Yayin da suke ganawa da manema labarai bayan taron da suka yi a birnin Paris, wanda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jagoranta, shugaban Chadi Idris Deby, yace suna bukatar isassun kudade wajen gudanar da ayyukan cigaba.

A na shi jawabi shugaban jamhuriyar Nijar, Muhammadou Issofou cewa yayi, abin takaici ne yadda dubban matasa ke mutuwa a teku, a kokarinsu na isa turai, inda yace sun gaji da yadda kasashen Turan ke yi musu alkawurra ba tare da cikawa ba.

To sai dai, yayinda yake zantawa da sashin Hausa na RFI Dr Maina Bukar Kartey na jami’ar Yammai da ke Nijar yace ba a nan matsalar take ba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

313total visits,1visits today


Karanta:  Siera Leone: Zabtarewar laka ta kashe mutum 300

Leave a Reply

Your email address will not be published.