Cinikin Malabu: Majalisa za ta gayyaci Jonathan don bincike

Ana zargin an yi ba daidai ba da dukiyar kasa lokacin shugabancin Goodluck Jonathan

Rahotanni daga Najeriya na cewa wani kwamitin bincike na Majalisar Wakilan Najeriya kan cikin rijiyar mai OPL 245 na dala biliyan 1.3 wadda aka fi sani da Malabu, ya ce zai tura wasikar gayyata ga tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.

Shugaban kwamitin, Razaq Atunwa, ya ce mambobin kwamitin sun umarci akawun majalisar ya rubuta wasikar gayyata ga tsohon shugaban Najeriyar.

A cinikin da aka fi sani da Malabu dai, manyan kamfanonin makamashi, Shell da ENI, sun biya dala biliyan 1.3 domin sayan daya daga cikin manyan rijiyoyin mai mafi daraja a Afirka.

Kwamitin ya ce zai gayyaci Mista Jonathan ne saboda shi ne shugaban Najeriya a lokacin da aka cimma cinikin, wanda kuma ake zargin cewar an yi sama da fadi da dala biliyan daya daga kudin cinikin.

Kwamitin ya kara da cewar sunan tsohon shugaban Najeriyar ya fito sosai a binciken da aka yi a Milan da ke kasar Italiya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

506total visits,1visits today


Karanta:  An kori 'yan sandan da 'suka wawushe gidan Jonathan'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.