Crystal Palace na shirin nada De Boer kociya

Crystal Palace ta ba wa tsohon dan wasan Holland Frank de Boer mai shekara 47, kociyanta kuma tattaunawa ta yi nisa kan kwantiragin da za su kulla.

De Boer zai gaji Sam Allardyce, wanda ya bar kungiyar bayan ya ceto ta daga faduwa a gasar Premier a kakar da ta kare.

De Boer wanda ya taka wa kasarsa Holland leda sau 112, ba shi da aiki tun lokacin da Inter Milan ta sallame shi a watan Nuwamba na 2016 bayan kwanaki 85 da kama aikin kocinta.

A tsakanin 2010 da 2016 De Boer ya yi kocin Ajax, inda ya dauki kofin gasar kasar sau hudu a jere daga 2011 zuwa 2015.

Ya ajiye aikin kwanaki kadan bayan ya kuskure kofin na biyar, wanda PSV Eindhoven ta yi nasarar dauka a rana ta karshe ta gasar a kakar 2015-16.

Ana ganin tsohon dan wasan bayan na Ajax da Barcelona da kuma Rangers yana ba wa ‘yan wasan da ya tarar a kungiya dama su nuna kansu kafin ya nemi sayo sababbi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

614total visits,1visits today


Karanta:  Ni Nake Bin Barcelona Kudi — Neymar

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.