Crystal Palace ta kori Frank de Boer

Crystal Palace ta kori kocinta, Frank de Boer bayan da ya ja ragamar kungiyar wasa biyar a kwana 77 da ya yi.

Palace tana ta 19 a karshen teburin, bayan da Burnley ta doke ta 1-0 a wasan mako na hudu a ranar Lahadi, kuma ta kasa cin wasa a karkashin De Boer.

Kungiyar wacce ta sanar da korar De Boer a shafinta na Intanet ta gode wa kocin kan yadda ya gudanar da aikin.

Kocin ya karbi aikin ne bayan da aka kare Premier ta 2016/17, inda ya maye gurbin Sam Allardyce.

A cikin watan Nuwamba Inter Milan ta kori De Boer bayan da ya yi kwana 85 a kan aiki.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1506total visits,3visits today


Karanta:  An fidda sunayen masu buga wa Najeriya gasar cin kofin duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.