Dan Masanin Kano Maitama Sule ya rasu

Allah ya yi wa Dan masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule rasuwa a ranar Litinin da safe bayan ya sha fama da jinya.

Wata majiya daga iyalansa ta tabbatarwa da BBC rasuwar, amma babu wani karin bayani zuwa lokacin wallafa wannan labari.

Ya rasu ne a kasar Masar inda ya yi jinyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Dan masanin Kano ya mutu yana da shekara 88 a duniya.

A shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama’a.

Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.

Har ila yau, gwamnatin Shagari ta nada shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.

A can ne ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.

A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu ‘yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama’a bayaninta.

Ya rasu ya bar ‘ya’ya 10 – maza hudu da mata shida.

Asalin Labari:

BBC Hausa

568total visits,1visits today


Karanta:  Buhari ya Kammala Tsara Kasafin Kudin 2018

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.