Daurarru 100 Sun Tsere Daga Gidan Yari

Sama da dauraru 100 ne suka tsere daga gidan yari a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo yayin wani mamakon ruwan sama, a cewar Daraktan Gidan Yarin Mutanade Nyongoli ranar Talata.

Mutum 119 da ake tsare dasu ne suka gudu daga gidan kason a garin Kabinda dake tsakiyar Congo a lardin Lomami ranar Litinin, a cewar ta Nyongoli.

Yace wasu mutum biyar daga cikin daurarrun wanda suka kusa gama zaman kason basu gudu ba sun zabi su cigaba da zama a sel dinsu.

“Tuni dai ‘yan sanda suka kama da dama daga cikin wadanda suka gudun”, in ji Nyongoli, ya kara da cewa yawanci daurarrun suna zaman sauraren yanke hukunci ne a gidan kason.
Ba a fiye samun guduwar daurarrun ba a Congo, inda aka samu tserewar daurarru 900 a gidan yari daya a arewacin lardin Kivu a watan Yuni bayan wasu ‘yan bindiga suka yiwa gidan yarin tsinke.

An kuma samu guduwar wasu daurarrun da dama a babban birnin Kinshasa a watan Mayu, inda wasu ‘yan kungiyar addini suka kai hari kurkuku suka kuma tseratar da daurarrun da yawansu yakai 4, 000 bisa kiyasi.

Rahotannin Kungiyoyin Kare ‘Yancin Dan Adam sunyi nuni da cewa yanayin da daurarrun ke ciki a kurkun bashi da inganci saboda yawansu da kuma jan lokaci da ake kafin yanke hukunci

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Vanguard, NANA

449total visits,2visits today


Karanta:  Me ya sa Osinbajo ke tsoron zakewa a mulki?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.