Di Maria ya yarda da laifin kin biyan haraji

Angel di Maria

Tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria ya amince ya biya tarar Euro miliyan biyu a kan tuhumarsa ta zambar kudin haraji.

Hukumomin Spaniya sun ce dan wasan zai amince da laifi biyu da ake tuhumarsa da su a lokacin yana Real Madrid, laifukan da suka danganci harkokin kudinsa, wanda a kan hakan ne zai biya kudin.

Dan wasan na Argentina mai shekara 29, wanda yanzu yake Paris St Germain na daga manyan ‘yan wasa da kociyoyi da hukumomin Spaniya ke binciken harkokin kudinsu.

Hukumomin suna zargin Di Maria da kauce wa biyan harajin da ya kai na euro miliyan 1.3 a kakar 2012-2013.

Laifuka biyun da zai amsa cewa ya aikata, suna da hukuncin zaman gidan yari ne na wata takwas kowanne, amma bisa dokar kasar, idan a karon farko ne mutum ya aikata laifin da hukuncinsa yake kasa da zaman kaso na shekara biyu, ba sai ya je gidan sarkar ba.

Kociyan Manchester United Jose Mourinho da dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo sun musanta irin wannan zargi da hukumomin kasar ke yi musu.

Asalin Labari:

BBC Hausa

343total visits,1visits today


Karanta:  Manchester United ta amince ta sayi Romelu Lukaku kan fan miliyan 75

Leave a Reply

Your email address will not be published.