Dogara Ya Zama Mamba na Dundundun a Kungiyar Lawyoyi ta Afirka

Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Hon. Yakubu Dogara ya zama Mamba na dundundun a Kungiyar Lawyoyi ta Afirka. Ita dai wannan kungiya ta hada manyan lawyoyi a nahiyar Afrika wadanda kanyi magana da harshe daya wajen ganin cewar fannin shari’a ya tsira da mutuncin sa domin cigaban nahiyar.

Kakakin Kungiyar Mista Robin da kuma shugaban Kungiyar Mista Hannibal sunce wannan ban girma da Kakakin Majalisar Wakilai ta Kasa Hon. Yakubu Dogara ya samu yazo ne sakamakon gudunmawa ta musamman da yakan bayar wajen tafi da harkar majalisa dama ci gaban al’umma baki daya.

Yakubu Dogara a yayin da yake karba gami da amincewa, ya bayar da tabbacin cewar zai tsaya tsayin daka don ganin cewar ya bayar da babbar gudunmawa a fannin shari’a da cigaban ita wannan kungiya domin kawo sauyi mai alfanu a nahiyar ta Afrika.

Ya kara da cewa yana mai godiya ta musamman da wannan girmama da aka bashi Mamba na dundundun. Don haka ya amsa zai bayar da babbar gudunmawa don tabbatar da jagoranci man inganci.

1760total visits,1visits today


Karanta:  EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.