EFCC Ta Tabbatar Da Shirin Taso Keyar Madueke Zuwa Najeriya

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, EFCC ta tabbatar da shirin taso keyar tsohuwar Ministan mai, Diezani Aison Madueke daga Ingila zuwa Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan Najeriya sun bukaci hukumomi da su taso keyar tsohuwar Ministar saboda zargin ta da cin hanci da rashawa.

Tuni dai, kotu da mallaka wa gwamnatin Najeriya wasu kadarori na biliyoyin Naira da aka kwato daga hannun Madueke bayan ta tara su ta haramtacciyar hanya.

Shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ce, suna kan gudanar da bincike game da taso keyarta kuma wadanda ake zargi da cin hanci ba za su tsira daga fuskantar hukunci ba.

Magu ya kara da cewa, a yanzu, sun kai matsayin da babu wanda zai dakatar da su a yakin da su ke yi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, kuma suna wannan aikin ne don amfanin al’ummar da za ta zo nan gaba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

663total visits,1visits today


Karanta:  Wani jami'in EFCC ya kubuta a hannun 'yan bindiga

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.