Ethiopian Airlines na son karbe iko da Arik Air

Kamfanin jiragen sama na Ethiopian Airlines na tattaunawa domin duba yiwuwar karbe ragamar gudanar da kamfanin Arik Air na Najeriya wanda ke fama da matsaloli.

Gwamnatin Nigeria ta karbe ragamar gudanar da kamfanin a farkon bana bayan da ya sanar da yin gagarumar asara.

Wani babban jami’i a kamfanin Esayas Woldemariam, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tattaunawar ta biyo bayan bukatar hakan ne da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta Najeriya ta yi masa.

“Hakika muna so kuma a shirye mu ke mu karbi ragamar gudanar da Arik Air,” a cewarsa.

Ethiopian Airlines shi ne kamfanin zirga-zirgar jiragen sama mafi samun riba a nahiyar Afrika, a cewar jaridar Business Daily.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1113total visits,1visits today


Karanta:  Ban Mayar Da Osinbajo Saniyar-Ware Ba — Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.