An fara kewaye Jami’ar Maiduguri da ramuka don kariya daga Boko Haram

Hukumomi a Najeriya sun fara aikin zagaye Jami’ar Maiduguri da ramuka don kare makarantar daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

Sanarwar fara aikin wanda zai kai nisan kilomita 27 kuma zai ci naira miliyan 50 ta zo ne kwana guda bayan wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari jami’ar, inda suka kashe kansu da kuma wata ma’aikaciya.

A ranar Litinin ne Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya sanar da aikin fara gina ramummukan, yayin da ya kai ziyara jami’ar don duba ta’adin da maharan suka yi.

Gwamnan ya ce za a haka ramummukan ne domin dakile duk wani yunkuri kai harin da za iya fuskanta a jami’ar nan gaba.

Sai dai bai bayyana taswon lokacin da za a kammala aikin ba.

Har ila yau, Shugaban Jami’ar Aliyu Shugaba ya ce sun gabatar da aikin ginin wata doguwar katanga wadda za ta kewaye jami’ar a wani mataki na kara kare jami’ar daga hare-hare.

Jami’ar Maiduguri dai ta zama wani wuri da ke yawan fuskantar hare-haren ‘yan Boko Haram a ‘yan watannin nan.

Asalin Labari:

BBC Hausa

485total visits,2visits today


Karanta:  Gwamnan Jihar Neja Ya Kara Korar Kwamishinoninsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.