Farashin Man Fetur Ya Sauko, Inji Kamfanin NNPC

Faduwar farshin ta fi kamari a ma’adanan mai masu zaman kansu inda farashin ya fadi zuwa Naira 130 ko Naira 131a kowace lita inda ’yan kasuwa za su sami ribar Naira bakwai.

Kamfanin Man Fetur na NNPC ya ce farashin man fetur ya sauko daga Naira 133 zuwa Naira 133 da digo 28 a kowace lita a mafiyawan daffon ajiyar mai inda hakan yake nuna cewa ’yan kasuwa za su sami ribar Naira hudu da digo 72.
Faduwar farshin ta fi kamari a ma’adanan mai masu zaman kansu inda farashin ya fadi zuwa Naira 130 ko Naira 131a kowace lita inda ’yan kasuwa za su sami ribar Naira bakwai.
Kamfanin NNPC ya bayyana cewa sakamakon haka farashin man ya fadi warwas daga Naira 145 a kowace lita zuwa tsakanin Naira 142 zuwa Naira 143 a kowace lita a wasu gidajen man da ke kasar nan.
Aminiya ta lura cewa masu motoci da ke da tankin mai da ke cin lita 60 a misali za su sami ribar Naira 180 duk lokacin da suka cika tankinsu makil.

 

Asalin Labari:

Aminiya

383total visits,1visits today


Karanta:  Sojoji sun ceto masu bincike da Boko Haram suka yi wa Kwanton Bauna

Leave a Reply

Your email address will not be published.