Fasto 2 Sun Gurfana Gaban Kotu Bisa Zargin Satar Yarinya ‘Yar Shekara 2

‘Yan sanda a Legas ranar Laraba sun gurfanar da wasu fasto biyu, Dorothy Ekutosi me shekara 51 da Asekameh Victor me shekara 27 gaban wata Kotun Majistire dake Ikeja bisa zargin satar wata yarinya ‘yar shekara biyu da haihuwa a cikin wata kasuwa

Wadanda ake karar wadanada har yanzu ba a bayyana adireshinsu ba suna fuskantar shari’a kan tuhuma guda biyu da suka hada da makirci da sata.

Dan sanda mai gabatar da kara Sifeto Clifford Ogu ya fadawa kotu cewa wadanda ake karar sun aikata laifuffukan ne ranar 29 ga watan Agusta a kasuwar Abule dake Ajao cikin jihar.

Yake cewa wadanda ake karar sun shirya makirci da kuma sace yarinyar a kasuwar ba tare da sanin mahaifiyar yarinyar ba wadda daya daga cikin ‘yan kasuwar ne.

“An kama mutanen biyu ne tare da taimakon makotan mahaifiyar yarinyar na cikin kasuwar lokacin da suka kama wadanda ake zargin dauke da yarinyar zuwa gurin da ba a san ko ina ne ba,” a cewar mai shigar da karar.

A cewarsa, wadannan laifuffukan sun saba da sashi na 287 da 409 na Kundin Manyan Laifuffukan Jihar Legas na shekarar 2015.

Wadanda ake karar sun musanta zargin da ake musu.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN sun rawaito cewa sashi na 287 ya bayyana hukuncin daurin shekaru uku kan laifin sata.

Babban Alkaliyar Kotun Majistiren Mrs Taiwo Akanni ta bada belin wadanda ake zargin kan kudi N100,000 kowannensu da mutane biyu da zasu tsaya musu.

Akkani tace dole ne wadanda zasu tsaya musun su kasance ‘yan uwan wadanda ake karar ne kuma sunada takardar biyan Gwamnati Jihar Legas harajin shekara uku.

Karanta:  An yi hatsaniya tsakanin magoya bayan Buhari da masu son ya sauka

Ta daga  karar zuwa 20 ga watan Satumba don cigaba da sauraro.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

246total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.