Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Shugaban Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari, watau Amata Alhaji Ado Bilyaminu, wanda ya nuna jin dadinsa na kaddamar da wannan asusu, inda ya bayyana cewa ‘yan kasuwar Sabon Gari masu dimbin yawa sun yi mummunar asarar dukiyoyinsu wanda sakamakon wannan gobara da yawansu ba sa zuwa kasuwa, saboda komai nasu wuta ta cinye, kuma babu wani jarin da za su iya komawa kasuwanci.

Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani asusu domin tara kudi don  tallafa wa ‘yan kasuwar da iftila’in gobara  ya shafa,  kuma a lokuta daban-daban  a kasuwanni guda biyar da ke jihar, watau kasuwar Sabon Gari da kasuwar Kurmi da kasuwar Singa kasuwar garin Gwarzo da kuma kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke Farm Centre.

An kuma samu gudummawa ta Naira biliyan biyu, inda ita kanta gwamnatin jihar ta ba da Naira miliyan 500  yayin da shi ma babban mai kadammarwa, kuma shugaban rukunin kamfanonin  dangote, Alhaji  Aliko dangote  ya ba da gudummawar Naira miliyan 500, inda kudin suka tashi Naira biliyan daya yayin da aka hada biliyan daya daga sauran al’umma da kungiyoyin kasuwanni da sauran wurare, wato dai jimlar kudin suka tashi Naira biliyan biyu.

Wakilinmu ya zagaya kasuwannin da gobarar ta shafa, domin jin yadda suka ji dangane da wannan kokari na gwamnati da sauran al’umma da suka ba da tallafin su, inda kowace kungiyar kasuwa ta yi bayani kan al’amarin tare da yin tsokaci daban-daban kan yadda ya kamata a raba wadannan kudi ga wadanda iftila’in gobarar ya shafa.

Shugaban  Hadaddiyar  kungiyar ‘yan kasuwar Sabon Gari,  watau  Amata Alhaji  Ado  Bilyaminu,  wanda ya nuna jin dadinsa na kaddamar da wannan asusu, inda ya bayyana cewa ‘yan kasuwar Sabon Gari masu dimbin yawa sun yi mummunar asarar dukiyoyinsu wanda sakamakon wannan gobara da yawansu ba sa zuwa kasuwa, saboda komai nasu wuta ta cinye, kuma babu wani jarin da za su iya komawa kasuwanci.

Don haka ne ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta himmatu wajen raba wannan tallafi da aka tattara, ta yadda kowa zai dawo kasuwa ya ci gaba da harkokinsa  kamar yadda aka saba. Sannan ya yi fatan cewa za a yi amfani da wakilai na ‘yan kasuwa wajen ba da tallafin  don cimma nasarar da ake bukata.

Karanta:  'Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?'

Haka kuma ya yaba wa ‘yan kasuwar ta Sabon Gari bisa hakuri da juriya da suka nuna kafin kaddamar da wannan asusu na tallafa musu, inda kuma ya ba da tabbacin cewa kungiyar su za ta tsaya sosai wajen ganin kowane dan kasuwa da aka tantance ya samu  tallafin  domin ci gaba da  kasuwancinsa.

Alhaji  Ahmed  Sadik Musa Boy, wanda jami’i ne a kungiyar kasuwar sayar da wayar hannu ta Farm Centre ya shaida wa Aminiya cewa, tallafin ya zo daidai lokacin da ake bukatarsa, kuma suna fata za a bai wa wadanda gobarar ta shafa taimakon da ya dace maimakon yunkurin da ake yi na sake fasalin wannan kasuwa, domin a cewarsa ‘yan kasuwar suna cikin wani yanayi na bukatar samun wannan tallafi ta yadda za su koma harkokinsu na yau da kullum.

Ya ce a wannan kasuwa kadai akwai mutane fiye da dubu uku da suke cin abinci a wurin  a kullum, amma da yawansu sun zamo marasa jarin yin sana’arsu kamar yadda abin yake kafin wannan jarrabawa ta gobara, sannan ya yi fatan cewa tallafin da za a bayar zai zamo alheri ga dukkanin wadanda suka same shi domin sake farfado da kasuwancinsu.

Shi ma  a nasa tsokacin a madadin daukacin ‘yan kasuwar Singa, sakataren kungiyar ‘yan kasuwar  Alhaji  Abba Mohammed  Bello ya ce kaddamar da asusun tallafin ya yi daidai, amma abin da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar ya yi kadan idan aka dubi irin yawan ‘yan kasuwar da suka tafka asara a lokutan iftila’in gobarar da aka jera a kasuwannin jihar.

Ya ce ‘yan kasuwa su ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki a kowace kasa ta duniya, don haka suna bukatar tallafi ingantacce domin bunkasa cinikayya da samar da  karin  guraben ayyukan yi masu tarin yawa, don haka  yana da kyau Gwamna Dokta  Abdullahi  Umar  Ganduje ya dubi wannan bukata domin kara share hawayen ‘yan kasuwar Jihar Kano kamar yadda  Gwamnatin Jihar Legas da Kebbi suke tallafa wa ‘yan kasuwar su a kodayaushe.

Karanta:  Nigeria na Cikin Halin Murmurewa - Farfesa Sheka

Sannan ya shawarci gwamnati da ta kafa kwamiti  na mutane masu amana  irin su Alhaji Uba Zubairu  Yakasai, wanda shi ne zababben shugaban  kungiyar  ‘yan kasuwar  Singa  domin yin  aikin rabon tallafin, wanda zai kunshi shugabannin kungiyoyin  ‘yan kasuwa da mutane masu kima, kuma  wadanda   suka san kasuwaci domin  kauce wa son zuciya wajen ba da wannan tallafi,  sannan  ya  tunatar da gGwamna Ganduje  cewa  ‘yan kasuwa su ne  mafi rinjaye  cikin al’umma idan aka dubi yawansu a fadin Jihar Kano da kewaye, tare da  tabbatar da cewa idan  aka taimake su  ko shakka babu  su ne  za su kara bai wa gwamnatinsa  kuri’a mafi rinjaye a zabe mai zuwa cikin yardar Allah.

daukacin kasuwannin da wakilinmu ya ziyarta sun yi fatan cewa za a danka aikin ba da tallafin ga mutane nagari, wadanda ba za a hada kai da  su  a cuci  wadanda ya kamata a tallafawa, ba tare da yin kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta ci gaba da shirinta na inganta kasuwanci, ta hanyar kyautata yanayin  manyan  kasuwannin da ake da su a jihar, kamar yadda ake yi a kasuwar Kantin Kwari.

 

Asalin Labari:

Aminya

927total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.