Filato: Mutane 19 Sun Rasa Rayukansu a Wani Harin Ta’addanci Da Aka Kai

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane 19 a wani hari da wasu da ba a tantance ba suka kai a kauyen Ancha dake yankin Miango na karamar hukumar Basa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato Peter Ogunyawo, ya shaidawa manema labarai cewa bakwai daga cikin wadanda aka kashen maza ne da mata shida da kananan yara shida, yayin da biyar din da suka sami raunuka ke karbar jinya a wani asibiti a Miango.

Peter Ogunyawo, ya ce maharani da ake kyautata zaton fulani ne sun kai hari a kauyukan inda suka bi gida-gida suka kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba lokacin da suke barci. Ya kuma ‘kara da cewa bai kamata jama’a su rika ‘daukar doka a hannunsu ba.

‘Yan sandan dai na zaton cewa kila harin ramuwar gayya ne bayan da aka kashe wani yaron fulani a kwanakin baya, wanda jami’an tsaro sun damke mutane biyar dake da tuhuma da kisan kan.

A halin da ake cikin kuma gwamnatin Filato tayi tur da yunkurin wasu na ruguza zaman lafiyar da aka samu a jihar.

Asalin Labari:

VOA Hausa

305total visits,1visits today


Karanta:  Gwamnatin Jihar Taraba Tana Bin Gwamnatin Taraiya Sama Da Naira Biliyan 30

Leave a Reply

Your email address will not be published.