Fulani 54 aka kashe, 15 kuma sun bata a Kaduna – Miyetti Allah

Kungiyar Miyetti Allah ta musanta rahotannin da ake yadawa cewar mutane 34 ne aka kashe a tashin hankalin da ya faru baya-bayan nan a Karamar Hukumar Kajuru dake Kaduna, Sakataren kungiyar ya sanar da cewar mutane 54 ne, kuma guda 15 sun yi batan damo har yanzu ba a gansu ba.

Mataimakin Babban Sakatare na kungiyar, Ibrahim Abdullahi ya bayyanawa manema labarai a ranar Asabar a Kaduna, cewar mutane 500 wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara wadanda aka kashe mazajensu ko suka bata, na neman mafaka a Kajuru da Kasuwar Magani.

“Idan har ba a manta ba mun yi kira kan kisan gilla da aka yi wa wasu fulani su 4 a Karamar Hukumar Kujuru da ke Kaduna. A lokacin mun bayyana dalilan da ke janyo kisan rashin adalci da ake yi wa mutanen mu, wanda ya samo asali ne sakamakon garkuwa da ake da mutane wanda jama’ar Adara da Fulani ba su da hannu. Muna kira ga hukumomin tsaar da su yi abinda ya dace don gurfanar da masu wannan aiki ga shari’ah.” In ji Sakatare.

“Muna kuma kara kira ga jama’a da su kara hakuri, kuma ka da su dau doka a hannunsu”.

 

4358total visits,1visits today


Karanta:  Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.