Gobara Ta Kama a Kasuwar Masaka Dake Karu, Nassarawa

Wata gobara da ta farke da tsakar daren jiya Asabar ta yi sanadiyar salwantar dukiyoyi na miliyoyin nairori a kasuwar unguwar Masaka dake yankin Karamar Hukumar Karu a jihar Nasarawa.

Majiyar Jaridar Rariya ta bayyana cewa an shafe awanni da dama kafin jami’an kashe gobara daga babban birnin Abuja su iso domin shawo kanta.

Jami’an ‘Yan sanda shiyar Karu ta yi nasara cafke wadan su mutane a yayin da suke yunkurin kwashe kaya suna izuwa gidajen su a yayin da gobarar take ci.

3259total visits,1visits today


Karanta:  Gobarar tankar mai ta kashe mutane a Cross River

Leave a Reply

Your email address will not be published.