Gobara ta tashi a kurkukun Kuje na Abuja

Wata gagarumar gobara wadda ta lashe gine-gine da yawa ta tashi a cikin kurkukun Kuje, dake Abuja. Gobarar wadda ta fara da misalin karfe 10:45 na safe, ta yi barna matuka.

Wata kungiya wadda ta kira kanta da ‘Mai Yaki da rashin adalci kan fursunoni ta Najeriya (PAIN), ta dauki alhakin tashin gobarar. PAIN ta bada wannan rubutaccen sako ne ta hanyar takardar da ta manna a babban allon saka sakonni na gidan yarin, kafin ma’aikata su cire shi.

PAIN ta kara da cewar wannan gobarar na nufin janyo hankalin duniya kan halin takaici da gidan yarin ke ciki da kuma rashawa da ta yi kaka-tutu tsakanin ma’aikatan gidan yarin.

Jawaban sun kara haske kan mutuwar baya-bayan nan ta wani dan fursuna mai suna Samuel Mba, a ranar Talatar 27 ga watan Yuni. Dan fursunan da ke jiran shari’a amma aka ajiye shi sama da shekara hudu ba wani cikakken bayani. Kungiyar ta jefa alhakin mutuwar Mba da sauran fursunoni da suka rasu kan halin ko-in-kula, rashawa da rashin cikakkun tsarin kulawa da lafiya, magunguna da taimakon gaggawa ga fursunoni.

PAIN ta kara da cewar duk da makudan kudaden da ake warewa don tafi da al’amurran gidajen yari, ana tilastawa fursunoni siyan maganguna ko neman lafiya a wajen gidan yari idan hakan ta kama. Halayyar da kan janyo wadanda ba su da halin yi wa kansu, rasa rayukansu a lokatai da yawa.

 

 

 

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Sahara Reporters

5006total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.