Gobara ta tashi a sansanin ‘yan gudun hijirar Syria

Akalla mutum daya ne ya mutu bayan wata gobara da ta tashi a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke tsaunin Bekaa da ke gabashin Lebanon.

Rahotanni farko sun ce mutum uku ne suka mutu sanadiyyar gobarar.

Al’amarin ya faru ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kusa da garin Qab Elias a tsaunin Bekaa.

Ma’aikatan ba da agaji na kungiyar Red Cross sun ce ‘yan gudun hijira 700 aka kwashe daga sansanin.

Wani ganau ya ce uku ne cikin tantuna 93 da ake da su a sansanin suka rage.

Kasar Lebanon ta yi wa ‘yan gudun hijiran Syria miliyan daya rijista, amma ana ganin yawansu ya kai kimanin miliyan daya da rabi a cikin kasar.

Galibin ‘yan gudun hijiran da suka guje wa shekara shida na yaki a Syria suna zaune ne a wasu sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da ke kasar.

Asalin Labari:

BBC Hausa

478total visits,1visits today


Karanta:  Sojojin Syria Sun Sanar da Tsagaita Wuta a Gabashin Ghouta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.