Gobarar tankar mai ta kashe mutane a Cross River

Hukumomi a Najeriya sun fara bincike kan fashewar wata tankar gas a jihar Cross River da ke yankin Niger Delta mai arzikin mai.

‘Yan sanda sun ce a kalla mutum goma ne suka mutu, bayan fashewar wata tankar mai a jihar Cross River, lamarin ya janyo gobara.

Yayin da wasu mutane fiye da goma ne kuma aka bayyana cewa sun samu munanan raunuka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da tankar mai ta fashe kuma gobarar da ta janyo ya ke sanadiyyar mutuwar mutane a Najeriya ba.

A wasu lokutan lamarin kan kazanta ne idan mutane sun je domin diban man da ke zuba daga motar, kuma gobara ta tashi da su.

Asalin Labari:

BBC Hausa

645total visits,1visits today


Karanta:  Gobara Ta Kama a Kasuwar Masaka Dake Karu, Nassarawa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.