Gwamnatin Jihar Borno ta fara gina ganuwar jami’ar Maiduguri

An fara aikin gina ganuwar jami’ar Maiduguri don hana masu kai harin kunar bakin wake a jami’ar kaiwa cikin harabar jami’ar. Hukumar jami’ar Maiduguri tana gina wannan ganuwar ce da taimakon gwamnatin jihar Borno.

An fara aikin gina ganuwar jami’ar Maiduguri don hana masu kai harin kunar bakin wake a jami’ar kaiwa cikin harabar jami’ar. Hukumar jami’ar Maiduguri tana gina wannan ganuwar ce da taimakon gwamnatin jihar Borno.

Daga watan Janairun wannan shekara jami’ar Maiduguri ta fuskancin harin yan kunar bakin wake sau goma daga yayan kungiyar Boko Haram. Hukumar jami’ar tana kyautata zaton wannan ganuwar zata taimaka wurin tabbatar da tsaro a jami’ar.

Komishinan ayyuaka da sufuri na jihar Borno Alhaji Adamu Lawan yace duk da cewar wannan jami’a ce ta gwamnatin tarayya amma suna da alhakin kare dalibai dake karatu a jami’ar musamman daliban kasashen waje. Ya kara da cewar gwamnatin jihar Borno tayi alkawarin gina wannan ganuwa mai tsawon kilomita goma don haka wajibin ta ne ta cika wannan alkawari.

Gwamnatin jihar ta bada bulo dubu dari biyu da suminti mota uku kuma an riga an bada Naira miliyon ashirin don fara wannan aiki. Ana sa ran kamala wannan ginin tsakanin watanni uku a cewar kwamishinanan ayyuka da sufuri na jihar Borno Alhaji Adamu Lawan.

Asalin Labari:

VOA Hausa

546total visits,3visits today


Karanta:  'An kashe 'yan Nigeria 97 a Cameroon'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.