Gwamnatin Nigeria ta Ayyana ‘Yan IPOB a Matsayin ‘Yan Ta’adda

Gwamnatin Najeriya ta ayyana kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biafra a matsayin kungiyar ‘yan-adda.

Tun farko dai rundunar sojan kasar ta yi irin wannan shela daga bisani kuma ta janye bayan da wasu suka yi ta suka da cewa ba ta da hurumin yin hakan kai-tsaye.

Sai dai a baya kungiyar ta musanta hakan, inda ta ce ita ba kungiyar ‘yan ta’adda ba ce.

Gwamnatin Najeriyar dai ta bayyana cewa yanzu ta samu izinin Babbar Kotun tarayya da ke Abuja, bayan da ta kai batun ga kotu cikin gaggawa domin samun sahalewar kotun bayan da Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan takardar haramta kungiyar.

Ministan sharia’a kuma Babban lauyan gwamnati, Abubakar Malami, ya tabbatar wa BBC cewa izinin kotun ya ba su damar ayyana kungiyar a matsayin ta ‘yan ta’adda.

161total visits,3visits today


Karanta:  Hukumar Kula da Lamuran Sufuri Zata Kawo Tsimin Kudi

Leave a Reply

Your email address will not be published.