Gwamnatin Tarayya Tayi Taron Gaggawa Kan Rikicin Mambilla A Jahar Taraba.

Hafizu Ibrahim hadimin mukaddashin shugaban kasa ne ya bayyana haka, bayan zaman da aka yi kan wannan batu.

Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbajo, ya kafa kwamitin bincike kan rikicin Taraba.

Parfessa Osinbajo, yayi ta’aziyya ga iyalan wadanda wannan rikici na tsaunin Mambilla ya shafa.

Babban hadimin mukaddashin shugaban kasa Hamisu Ibrahim, wanda ya bayyana haka, yace Parfessa Osibanjo, ya gana ne da shugabannin hukumomin tsaro tareda Gwamnan jahar Darius Isiyaku, da zummar gano bakin zare.

Da yake sharhi kan yawa-yawan tashe tashen hankula a arewacin kasar, Kabiru Danladi Lawunti, yace rashin hukunta wadanda suke tada wadannan fitintinun shi yasa ake ci gaba da fuskantar. Kamar yadda ake gani a jihohin Kaduna, da Flato, da Nasarawa, da Benue da Taraba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

155total visits,2visits today


Karanta:  Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published.