Gwamnatocin kasashen Arewacin Afrika na fargaban bazuwar mayakan ISIS a kasashensu

Yyinda kungiyar ISIS ke asarar yankunan da ta mamaye da a kasashen Syria da Iraq, kasashen Arewacin Afirka su na tsoron kada mayakan ISIS din su soma kwararawa zuwa yankinsu su tada hargitsi kamar yadda ake gani a Libya da Afghanistan

Yayin da kungiyar IS ta ke rasa mafi yawan yankunan da ke hannunta da kuma karfin ikonta a Syria da Iraqi, gwamnatocin kasashen yankin Arewacin Afirka, sun ce suna fargabar dawowar mayaka daga fagen yaki a Gabas ta Tsakiya, Ka iya haifar da rikici a yankunansu.

“Yankin na fuskantar barazana… idan mayakan suka dawo,” inji Ministan harkokin wajen Algeria, Abdul Qader Messahel, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Birnin Alqahira.

A ‘yan kwanakin nan, rahotannin sun yi nuni da cewa, akalla mayakan kasashen waje 5,600 ne suka baro fagen yaki bayan da aka samu galaba akan IS a Syria da Iraqi.

Daruruwan mayaka daga kasashen Arewacin Afirka, da suka hada da Tunisia da Morocco, sun riga sun koma kasashensu, a cewar wani rahoto da Cibiyar Soufan ta fitar, wacce ke da hedkwata a Birnin New York, take kuma bibiyan al’amuran da ke faruwa a yankin.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1724total visits,1visits today


Karanta:  Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.